Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Cin Kofin Afirka Ta Zo Da Ba Zata


Jiya, a rana ta biyu da fara gasar cin kofin kalubalenka na Afrika, ‘yan maza sunji jiki, cikinsu harda Namibia wacce ta sha kashin ci 5-1 a hannun Morocco.

Wannan yassa Morocco din ta bi bayan Ghana a matsayin kasashen dake da maki ukku-ukku koda yake ma yawan kwallayen Morocco sun zarce na Ghana din, tunda Ghana ci 2-1 tayi wa Guinea ranar farko da soma gasar.

A rukmunin B ne kuma Super Eagles na Nigeria suka fara jin ba dadi bayan da Elephants na Cote d’Ivoire suka rakkada musu ci 1-0 a birnin Sekondi. Har ila yau abin mamaki ya faru jiya a rukuni na biyun, inda Mali ta caccaka Junhuriyar Benin da ci 1-0 (wannan wasan ma an jinkirta shi saboda daukewar wutar lantarki.

A yau ma akwai gwabzawa sosai don a yau din ne kasar Masar (wacce ke rike da kofin) zata kara da Kamaru, yayinda Zambia ma zata nemi kece renin dake tsakaninta da Sudan.

XS
SM
MD
LG