Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Girgizar Kasa A Pakistan,Akalla Mutane Dari Da Sittin Sun Halaka.


Jami'an Pakistan sunce girgizar kasa data auku a kudu maso arewacin kasar ta kashe akalla mutane 160,kuma suna jin wannan adadi zai haura ganin masu aikin ceto sun fara tonon karkashin gine gine da suka rushe, domin neman wadanda suke raye,da kuma wadanda suka halaka.

Hukumar kula da yanayin kasa ta Amurka tace girgizar mai karfin awo 6.4 ta auku ne kilomita 100 daga arewa maso gabashin Quetta,fadar lardin Beluchistan,dab da Asubahi Laraban nan. Girgizar ta rusa gidaje ginin laka a kauyuka takwas, can nesa kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan,wacce ta razana mazauna kauyukan da suka gudu suka hallara wuri guda cikin sanyi suna dakon agaji.

Jami'ai suna kiyasin akalla mutane dubu 12 ne ahalin yanzu suka rasa gidajensu. Wani jami'in gunduma a Beluchistan,Sohail ur Rahman, ya gayawa wata kafar yada labaru cewa girgizar kasar ta rusa daruruwan gidaje ta halaka akalla mutane 80 a yankin nasa kadai.

XS
SM
MD
LG