Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Harbe Wani Ba Amerike  Da Matukinsa Har Lahira A Peshwar.


'Yansandan Pakistan sunce wasu 'yan bindiga sun harbe wani Jami'in Amurka mai aikin tallafi shi da matukinsa a yankin arewa maso yammacin kasar mai fama da rigingimu.

'Yansanda sunce anyiwa jami'in da matukinsa kwanton-bauna yau Laraba a unguwar da Jami'ar birnin take a Peshwar,fadar lardi dake arewa maso yammaci. Ofishin jakadancin Amurka yaki ya fayyace Jami'in,wadda Jami'an tsaro sukace yana aiki ne gameda ayyukan raya yankin na Kabilu. Zuwa yanzu babu mutum ko kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.

Ahalin yanzu kuma wani dan kunar bakin wake da mota ya kashe sojoji biyu,a hari da ya kai kan wata cibiyar soji a yankin arewa maso yammaci mai fama da rigingimu.

XS
SM
MD
LG