Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Yobe Ta kafa Dokar Hana Aure Ba Tareda An Auna Jini Ba


Gwamnatin Jihar Yobe dake arewa maso gabshin Najeriya ta kafa dokar da zata bukaci dukkan wadanda suke da niyyar aure cikin jihar su auna jini domin tabbatarda lafiyar su,musamman gameda cutar kanjamau ko sida.

Kwamishinan ma'aikatar addini,Alhaji Habu Dauda ne ya tabbatarda haka a hira da ya yi da wakiliyar sashen Hausa,Sa'adatu Mohammed Fawu. Kwamishinan yace,shirin zai sami nasara tareda taimakon majalisar sarakunan gargajiya,daga kan sarakunan har zuwa masu unguwa.

Da suke magana kan wan nan sabuwar doka,masu rajin hana yaduwar cutar, da ma wadanda ke dauke da ita,duk sun yaba da dokar. Sunce zata taimaka sosai wajen dakile yaduwarta ta auratayya ba tareda gwaji ba.

XS
SM
MD
LG