Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nepal Ta Cimma Yarjejeniya Da Yan Tawayen Mao


Dubban mutane ne suka bazu a titunan Nepal, domin murnar yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnatin kasar ta cimma da ‘yan tawaye masu akidar tsohon shugaban kasar Sin Mao Tse Tung.

Shugabannin kasar sun baiyana Laraba a matsayin hutu, domin bikin yarjejeniyar, wadda ta kare yakin kimanin shekaru goma, inda fiye da mutum dubu 13 suka salwanta.

Hatta sarki Gyanendra a wata ya bayar da sanarwa , inda yake goyon bayan yarjejeniyar, duk da cewa ta ragewa sarautar gargajiyar kasar ikon fada a ji.

Shugabannin kasashen duniya, cikinsu har da na Indiya, Birtaniya, Amurka, da Majalisar Dinkin Duniya duk sun jinjinawa yarjejeniyar.

A karkashin yarjejeniyar dai, ‘yan tawayen na Mao zasu takaita zirga zirgar mayakansu iya sansanonin ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan zai ci gaba har sai an gudanar da zaben majalisar da zata shata sabon tsarin mulki, wanda zai samawa sarakunan gargajiya matsayi.

XS
SM
MD
LG