Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Habasha Ta Kai Farmakin Bom A Magadishu


Mazauna birnin Mogadishu sunce a kalla jiragen yakin Habasha guda biyu sun keta sararin samaniyar birnin, inda suka jefa bama-bamai kan babbar tashar saukar jiragen sama.

Wani ma’aikacin Gidan Rediyon Shabelle ta Mogadishu, Mohammed Amin Sheikh Adow, ya shaidawa Muryar Amurka cewa wannan hari ya raunata wata mace, ya kuma lalata wani bangare na filin saukar jiragen saman. Adow yace wannan hari ya jefa al’ummar Mogadishu cikin rudu da damuwar abin da zai iya faruwa gobe. Yace "halin da ake ciki kullum sai kara tabarbarewa yake yi. Jama’a na tsoron makomarsu a gabe. Babu wanda yake tsammanin Habasha zata kawo wannan hari har birnin Mogadishu".

Adow yace Masu Kishin Islama, suna ta kira ga al’ummar Somaliya da su kwantar da hankulansu, kuma suyi damarar yakin kwatar kai, daga mamayar sojojin Habasha kimanin dubu 30 dake Kasarsu a halin yanzu.

Masu kishin Islaman dai, sun kwace mulki a Mogadishu kimanin watanni bakwai da suka wuce, kuma suka rika dannawa har saida suka kwace fiye da rabin kudanci da tsakiyar Somaliya. Wannan nasara ta Masu kishin Islaman, da barazanarsu na kwace wani yanki na Habasha su hade shi da kasarsu ta Somalia, shine ya shigar da Habasha cikin fadan, domin ta taimakawa gwamnatin rikon kwarya mai goyon bayan kasashen duniya, amma mara tagomashi a cikin gida, wadda ke da sansani a Baidoa, kilomita 250, kudu maso gabashin Mogadishu.

A halin yanzu dai fada ya barke tsakanin dakarun gwamnati tare da goyon bayan Habasha, da kuma masu kishin Islama a wajen Baidoa. Fadan da aka gwabza a satin da ya gabata dai, yayi sanadiyyar raunata dimbin mayaka daga bangarorin biyu.

XS
SM
MD
LG