Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwannin Hannayen Jari Suna Nuna Halin Rashin Sanin Tabbas A Yinin Talata


Kasuwannin saida hannayen jari suna nuna halin rashin sanin tabbas Talata,sakamakon dumbin hasara da suka tafka jiya litinin.

Kasuwannin shunkun Turai sun cira sama da fara hada-hadar yau,amma nan da nan kuma suka nosa kasa. Duk da haka zuwa tsakar ranar yau sun sake cirawa sama fiye da inda suka kwana a jiya litinin, inda kasuwannin na Turai suka tafka
babbar hasarar da basu taba ganin irin taba a yini daya.

Kasuwannin Asiya sun fara da mutuwar hannu,amma kuma suka fara haurawa,bayan da babban Bankin Australiya ya rage kudin fito fiye da abinda ake tsammani. Haka ma kasuwannin shunkun Taiwan Singapore da Korea Ta Kudu duk sun sami riba,amma ta China da India su faduwa suka yi

XS
SM
MD
LG