Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Da Fatah Sun Sabunta Yarjejeniyar Dakatar Da Tashin Hankula


Wani mai magana da yawun Gwamnatin Falasdinawa, Ghazi Hamad ne ya baiyana wannan yarjejeniya da yammacin ranar Litinin dinnan. Ministan Yada Labaran Falasdinawa Mustafa Bargouti yace gwamnati ta baza jami’an tsaro kan tituna, domin dawo da kwanciyar hankula a Zirin Gaza.

Mutum takwas ne suka mutu, fiye da hamsin kuma suka ji raunuka a arangamar da ake fa faman yi tun ranar Lahadi. Wannan fada dai ya ci gaba, duk kuwa da shiga tsakanin da kasar masar tayi, inda ta sasanta kungiyoyin biyu.

Da safiyar Litinin, Ministan Harkokin Cikin Gida na Falasdinawa Hani Kawasmeh ya sauka daga mukaminsa, inda yace Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Falasdinawa bata bashi cikakken ikon gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba. Ya soki kungiyoyin biyu na Hamas Da Fatah, wadanda yace sun kasa goyon bayan shawararsa ta sake fasalin hukumomin tsaron Falasdinawa.

Mustafa Bargouti, Ministan Yada Labarai yace fadan na baya-bayannan yana barazana ga dorewar gwamnatin ta hadin kan kasa wacce aka kafa watanni biyu kacal da suka shude, domin zai iya jawo rugujewarta.

Fadan ya barke ne a ranar Lahadi, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kashe wani kwamandan Dakarun Al-Aqsa mai goyon bayan Fatah, da direbansa. Kungiyar ta dora alhakin kisan a kan Hamas, amma Hamas din ta musa.

XS
SM
MD
LG