Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Gitta Sharuddan Aiwatarda Shirin Tsagaita Wuta A Gaza


Shugaban kungiyar jihadin falasdinawa ta Hamas Isma’ila Haniyeh, ya gitta wasu sharudda yau laraba kafin fara aiki da tsagaita wuta a Zirin Gaza tare da Isra’ila. Yace wajibi ne Isra’ila ta daina kai hare-haren kisan gillar da take yiwa Zirin Gaza, a kuma sake bude kan iyakokin Gaza da aka rufe tun watan Yunin da Hamas ta kwace mulkin yankin.

A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar Jam’iyyar Democrat a nan Amurka, Barack Obama, ya sami nasara a zaben tsaida yan takarar da aka gudanar jiya Talata a Mississippi, ya kuma kara babbar rata tsakaninsa da Hillary Clinton. Obama ya sami kashi sittin daga cikin dari, ita kuma Clinton nada talatin da tara.

Aran 22 ga watan gobe na Afrilu ne zaa sake karawa a Pennsylvania domin neman wakilai 158. Amma duk da haka kididdigar jin ra’ayin Amerkawa ta nuna cewar Hillary Clinton ce zata sami nasara idan an kammala zaben na Pennsylvania.

XS
SM
MD
LG