Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Dakon Sakamakon Zabe A Zimbabwe


‘Yan kasar Zimbabwe su na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da akayi cikin watan jiya, sakamakon da kafofin yada labaran kasar suka ce za a sake nan bada jumawa ba.

Wakilan hukumar zaben Zimbabwe sunce yau litinin, za a kammala sake kidaya kuri’u daga gundumomi ashirin da uku. Bayan kammala sake kidaya kuri’un ne jami’an suka ce za a gayyaci ‘yan takarar shugaban kasan ko wakilansu su tantance sakamakon zaben.

Kalaman daga shugaban hukumar zabe George Chiweshe, ya nuna cewa watakila hukumar ta gana da ‘yan takarar yau. Amma babu bayani kan anyi wannan taro zuwa sha biyun rana agogon Zimbabe. Kakakin Jam’iyyar ‘yan hamayya Nelson Chimasa ya gayawa Muriyar Amurka cewa Jam’iyyar bata da kwarin gwiwa kan sakamakon zabe da hukumar zata bayar.

Jam’iyyar MDC tace dan takarar ta Morgan tsvangirai ya doke shugaba Robert Mugabe a zaben shugaban kasa da akayi ranar 29 ga watan Maris. Hukumar zaben ta sha suka matuka daga kasashen duniya saboda kasa bayyana sakamakon zaben.

XS
SM
MD
LG