Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Zaman Rashin Tabbas A Masallacin Islamabad


Jami’an tsaron Pakistan sunyi harbin kashedi a kusa da masallacin nana da ake ta takaddama a kansa, a birnin Islamabad, a yayin da zaman dar-dar ke kara tsananta tsakanin ‘yan sanda da wadanda sukai mafaka a masallacin.

Shaidun gani da ido sunce a yau alhamis aka ji karar bindigogi, gami da sanarwa daga hukumomin tsaro, suna umartar daliban da su mika wuya. Wani jami’in tsaro yace an rushe katangar wani bangare na Lal Msajid, ko kuma jan Masallaci, kuma ‘yan sanda sun an harba barkonon tsohuwa cikin masallacin, amma sojoji basu kaiga shiga cikin masallacin ba tukuna.

Jami’an tsaron dai sun sami karin karfin guiwa, bayan sun kame shugaban masallacin, Abdul Aziz, yana kokarin guduwa, sanye da kayan mata. An kashe a kalla mutane 16 a wannan satin, a wani bata kashi tsakanin ‘yan sanda da dalibai a masallacin.

XS
SM
MD
LG