Accessibility links

Har Yanzu Tsugune Bata Kare Ba A Somaliya


Shaidun gani da ido sunce kwanson bama baman ya sauka a wata unguwa a birnin Mogadishu yau Alhamis. An kuma kai irin wannan hari a kalla sau uku, kan tashar jiragen ruwan kasar, a inda wasu dakarun Habasha suka yi sansani.

Babu dai wani tabbataccen bayanin wadanda suka kai wannan hari, amma dai jami’an gwamnati suna zargin hare haren baya a kan Kungiyar Islama ta Somaliya. Gwamnatin Rikon Kwaryae Somaliyan dai tana ta kokarin dakile tashe tashen hankula a babban birnin kasar, fiye da sati shida bayan korar masu kishin Islaman, tare da taimakon dakarun kasar Habasha.

Kunguyar Gamaiyar Afrika, wato AU tayi alkawarin aikewa da sojoji dubu takwas, domin taimakawa tabbatar da tsaro a kasar, kuma ayarin farko daga kasar Uganda zasu iya isa Somaliyan nan da ‘yan kwanaki.

XS
SM
MD
LG