Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Tana Zargin AMurka Ta Kai Hari Da Makamai Masu Linzami A Yankin Kasar.


Jami‘an Gwamnati a Pakistan sun bada rahoton cewar wani harin makami mai linzamin da ake zargin Amurka ce ta kai shi yau Juma’a da safe ya halaka mutane goma sha biyu a yankin nan da ake rikici na kan iyakar Arewa maso yammaci.

Jami‘an Gwamnatin Pakistan suka ce musamman aka shirya kai harin makami mai linzamin a kan ƙauyen Arewacin Waziristan tungar mayaƙan al-qaida da ’yan Taliban. Jami’an gwamnatin Pakistan suka ce anyi amfani da jirgin saman da ake sarrafa shi daga doron ƙasa wajen kai harin.

XS
SM
MD
LG