Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Rokoki Ya Girgiza Birnin Mogadishun Somaliya


Rahotannin dake shigowa daga babban Birnin Somaliya Mogadishu, sun nuna cewa wani harin bindigogin igwa ya girgiza birnin, kwana daya kadai bayan da sojojin kiyaye zaman lafiya na Kungiya tariyar africa suka fara isa kasar.

Shaidun gani da ido sunce wannan hari da aka kai da safiyar yau juma’a, yayi sanadiyyar rasuwar a kalla mutum shida. Suka ce manyan makaman sun sauka a tsakiyar birnin na mogadishu, a kalla daya kuma ya sauka a tashar jiragen ruwan birnin.

Jami’ai sun dara nauyin wannan hari a kan birbishin ‘yan gwagwarmaya masu kishin addinin Islama. Jiya talata jami’an sojin kasar Uganda su 30 suka sauka a Baidoa, mazaunin gwamnatin rikon kwarya.

Uganbda dai tayi alkawarin bayar da gudunmawar sojojin dubu daya da dari biyar, ga Gamayyar Afrika, dake son hada runduna mai sojoji dubu takwas.

Shugaban Rikon Kwarya Abdullahi Yusuf ya shaidawa majalisar kasar cewa ranar 16 ga watan gobe na Afrilu za a gudanar da wani taron hada kan kasa.

XS
SM
MD
LG