Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Isra'ila Ya Ci Gaba Da Kashe Falasdinawa


Yau aka shiga kwana na uku da fara wadansu munanan hare-haren Isra’ila kan yankin Falasdinawea na Zirin Gaza, inda yawan Falasdinawan da suka rasa rayukansu ya kai 310.

Shaidun gani da ido sunce jiragen saman yakin Isra’ila sunyi rugu-rugu da ma’aikatar harkikin cikin gida dake birnin Gaza, suka kuma harba a kalla bama-bamai biyar kan Jami’ar Islama ta Zirin gaza.

Isra’ila dai tace hare-haren, martani ne ga rokokin da masu kishin Islama suke ta faman aikawa daga Zirin Gaza, zuwa cikin yankunan ta. Ministar Harkikin Kasashen Wajen Isra’ila, Tzipi Livini ta musanta zargin cewa Isra’ila tana kokarin sake mamaye Zirin gaza ne.

XS
SM
MD
LG