Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake A Pakistan Ya Kashe Akalla Mutane Goma Sha Biyar


Akalla mutane 15 ne aka kashe wasu 40 kuma suka jikkata a harin kunar bakin wake da aka kai gidan wani wakilin Majalisa a gabashin Pakistan.

Jami’in ‘Yansanda,Khadeem Hussein,yace dan Majalisa Rasheed Akbar Nawani,dake Jam’iyyar tsohon PM Nawaz Shariff,ya jikkata a harin na yau litinin, da aka kai a gidan sa dake yankin Bhakkar,a lardin Punjab. Hussain yace dan harin kunar bakin waken ya tarwatsa kansa cikin taron magoya bayansa dan Majalisan.

Babu wanda ya fito nan nan da nan ya dauki alhakin kai wannan hari. Pakistan ta fiskanci tashe tashen hankula a makonnin nan. Jiya lahadi mayakan sakai na Taliban sun harba rokoki kan gidan wani sanannen dan siyasa a Arewa maso yammacin Pakistan.Babban Ministan kula da yankin,Amir Haider Khan Hoti bai ji rauni a harin ba,sai dai shaidu sunce rokokin sun yi lahani ga gidaje biyu dake makwabtaka da gidan Ministan.

XS
SM
MD
LG