Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Sayen Bangaren Wasu Bankuna Zai Yi Nasara, Inji Henry Paulson


Sakataren Baitul Malin Amurka Henry Paulson ya fada Laraba cewa yana da kwarin gwiwar shirin Gwamnati na ceto cibiyiyoyin hada hadar kudi zai sami nasara,amma zai dauki lokaci.

Yayi magana ne a tashoshin talabijin na ABC da NBC,kwana daya bayan da shugaba George Bush, ya bada sanarwar Gwamnati zata kashe dala milyan dubu metan da hamsin, domin sayen wani bangaren wasu Bankuna,kuma tayi lamuni kan karin basussuka da ajiyar Banki.

Irin wannan shirin ne ake dab da fara aiwatar wa a Turai danufin sake farfado da bada rance wadda ya cije,kuma ya jawo cikas ga kasuwanci,har yake neman ya durkusad da tattalin arzikin kasashen Duniya.

XS
SM
MD
LG