Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraq Da Birtaniya Zasu Taya Turkiyya Yaki Da Kurdawan PKK


Ministan harkokin Wajen Iraq, Hoshiyar Zebari yace gwamnatinsu zata taimakawa Turkiyya ta murkushe Kurdawa ‘yan tawaye, wadanda ke kai mata hare hare daga sansanoninsu dake Arewacin Iraq.

Ministan yayi wannan bayani ne a yau Talata a birnin Bagadaza, a wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi da takwaransa na Turkiyya, Ali Babacan. Zebari ya tabbatarwa da takwaran nasa cewa Bagadaza tana bayar da cikakken goyon baya ga kokarin Turkiyya na takaita abin da ya kira illolin ‘yan tawayen.

Yace Iraq ba zata kyale Jaa’iyyar Kurdawa ta PKK ta bata kyakkyawar dangantakar dake tsakaninta da Turkiyya ba.

A nasa bangaren, Babacan yace Turkiyya ta fi kaunar warware wannan matsala ta fuskar diplomasiyya, sulhu da matakan tattalin arziki. Yayi watsi da tayin tsagaita wuta da PKK tayi, a kokarinta na kautar da mamayar da Turkiyyan ke barazanar kai masu.

Daga birnin London kuma, Prime Ministan Ingila Gordon Brown yayi irin wannan taron manema labarai da takwaran aikinsa na Turkiyya Recep Tayyib Edorgan, inda yayi Alla-wadai da da take taken PKK, ya kuma yi alkawarin taimakawa wajen yin maganinsu.

XS
SM
MD
LG