Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraq Ta Mika Kokon Bara Ga Makwabtanta


Taron na kwana biyu ya sami halartar wakilan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar kasashen larabawa da kuma makwabtan na Iraq. Saidai Kasar Saudi Arabiya bata sami halarta ba.

A halin da ake ciki kuma, Prime Minista Nouri Al-Maliki yana birnin Tehran a halin yanzu, don don tattauna matsalar tsaro da shugabannin Iran.

A jiya Laraba, ya gana da Mataimakin Shugaban Kasar Iran din, Parviz Davoudi, wanda yace Iran tana iya bakin kokarinta wajen kyautata yanayin tsaron Iraq.

Mr. Maliki yana da dangantaka ta kusa ka kasar Iran, mai akidar Shi’a, kasar da kuma yayi zaman gudun hijira. Ana sa ran Nouri Al Maliki zai gana da Shugaba Mahmoud Ahmedinejad da kuma jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei.

XS
SM
MD
LG