Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinawa Sun Kama Turbar Yarjejeniya


Condoleezza Rice Tace tunda Shugaba Abbas da Prime Minista Olmert sun amince da sake zaunawa nan ba da dadewa ba, zata sake komata Gabas Ta Tsakiya a daidai lokacin zaman, don ta tabbatar an cimma wata yarjejeniya ta takamaimai.

Shugabannin biyu dai sun sake jaddada muradin ganin Amurka ta jagoranci yunkurin shawo kan matsalar dake hana ruwa gudu, ta kuma nemi goyon bayan kasa da kasa da na yankin da zai kai ga cimma zaman lafiya.

Rice tace tattaunawar ta kuma nuna bukatar sassan biyu na ganin bayan tashe tashen hankula. Shirin samar da zaman lafiyan, ya bukaci palasdinawa su daina kaiwa Isra’ila hari, Isra’ila kuma da taina gine ginen matsugunai a zirin Gaza, a matsayin daya daga cikin matakan kirkiro da kasar palasdinu.

Rice tace Mr Olmert da Mr Abbas sun tattauna a kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin guiwa a yankin Palasdinawa tsakanin Hamas da Fatah da aka cimma kwanan nan, sai dai bata bada wani karin haske kan yadda tattaunawar ta kasance ba.

XS
SM
MD
LG