Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ivory Coast Ta Kafa Sabuwar Hukumar Zabe


Gwamnatin Ivory Coast ta kafa sabuwar hukumar zabe, wani muhimmin mataki a kokarin warware rikicin siyasar kasar.

Jumma’ace jami’ai suka bayyana nada Youssouf Bakayo na jami’yyar hamayya PDCI a mtsayin shugaban sabuwar hukumar. ‘Yan hamayya sunce ba zasu shiga gwamnati ba sai shugaba Laurent Gbagbo ya sake maido da hukumar zaben da ya rusa kusan mako biyu da suka wuce. Shugaban kasan ya rusa hukumar zaben ce sabo da a cewarsa tana yi wa mutane rejista ba bisaka’ida ba.Haka kuma a lokaci guda ya rusa gwamnati,amma PM Guillaume Soro wadda tsohon dan tawaye ne ya bada sanarwar kafa sabuwar gwamnati ranar talata da ta wuce.

Kasar awani lokaci cikin kwanaki dasuka tana cikin rudani sabo da munanan zanga zanga na nuna adawa da matakai da shugaban kasan ya dauka.

XS
SM
MD
LG