Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar Ta Kori Gwamnatin Hamma Amadou


Wakilai 62 ne daga cikin 113 na majalisar suka kada kuri’ar amincewa da korar gwamnatin ta Hamma Amadu a jiya Alhamis.

Masu adawa da Prime Ministan sun zargeshi da hannu a abin kunyar da aka tafka na rashawa da barnatar da kudin ma’aikatar ilmi.

Ministocin Ilmi biyu aka daure saboda wani bincike da aka yi a lalitar gwamnati ya gano batan wadansu makudan kudade a ma’aikatar.

Jim kadan bayan kuri’ar, sai Malam Hamma Amadu yace ya amince da sakamakon da ya biyo baya, inda yace dimokradiyya ce ki yin aikinta.

Shekaru bakwai hamma amadu yayi a kan wannan mukami na Prime Minista.

Jamhuriyar Nijar tana kudancin hamadar sahara, kuma tana daga cikin kasashen da ake cewa suna fama da talauci a duniya.

XS
SM
MD
LG