Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamiyyar Democrat Ta Sha  Kaye A Zaben Cike Kujerar Marigayi Edward Kennedy A Jihar Massachussetts


A wani abin bazata, wani dan jam’iyyar republican ya lashe zaben kujerar senata a jihar Massachussetts, wacce kusan shekaru hamsin take hanun dan majalisar dattijai wadda ya fi kowa sassaucin ra’ayi, marigayi Edward kennedy.

Bayan an kidaya kashi 90 cikin dari a zaben na jiya talata,sakamako ya nuna cewa dan Republican wakili a majalisar dattijai jihar, Scott Brown ne, ya doke ‘yar takarar Democrat Martha Coakley,wacce itace Attorney janar ta Jihar.

Da yake magana ga gungun magoya bayansa masu sowa, Brown yace muriyar ‘yan jihar masu indipenda ta koka. Ya karrama marigayi senata Kennedy,kuma ya yi alkwarin zama magajinsa na kwarai. Haka kuma yace kujerar ta jama’ace ba mutum daya ko jam’iyya ba.

Brown zai kasance senata na jam’iyyar Republican na 41,a majalisar dattijai mai kujeru 100. Wan nan zai baiwa jam’iyyar marasa rinjaye su hana ruwa gudu kan shirin garambawul ga inshoran kiwon lafiya na shugaba Barack Obama,da sauran muradun gwamnatinsana cikin gida.

XS
SM
MD
LG