Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar SDF A Kamaru Tayi Watsi Da Zaben Majalisar Kasar


Jamiyyar SDF tace a yau dinnan zata shigar da koken nata, inda tace an tafka magudi a zaben, ga muguwar rashawa da cin hanci.

Shugaban Jam’iyyar John Fru Ndi ya shaidawa Gidan Rediyon VOA cewa koda yake dama ‘yan jam’iyyun adawa suna tsammanin magudi, sun shiga zaben ne musamman saboda su nuna wa jama’a irin wadannan matsaloli karara.

Jam’iyyar CPDM mai mulki tace wannan zargi na ‘yan adawa bashi da tushe, bashi kuma da makama.

Mutane basu fito sosai ba a wannan zabe, kuma shaidun gani da ido sunce mutane da yawa sun jefa kuri’a fiye da sau daya. An kyale wadansu kuma su jefa kuri’a ba tare da kati ba, kuma an hana yawancin masu kada kuri’a irin wannan kati.

Masu sharhi dai sunce sakamakon zabe zai baiwa Shugaba Paul Biya damar sabewa da mulkin da yayi shekaru 25 yana yi.

XS
SM
MD
LG