Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Gabashin Africa Suna Kokarin Kyautata Zumuncinsu


Shugabannin Kasashen Kungiyar ci gaban yankin Gabashin Afirka da ba’a jima da fadadawa ba, suna yin taron Koli a yau litinin domin tattauna kafa wata tarayya da za ta karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyar.

Shugaban Kenya Mwai Kibaki, da na Uganda Yoweri Museveni da na Tanzania Jakaya Kikwete da na Rwanda Paul Kagame da kuma na Burundi Pierre Nkuruziza, zasu tattauna a Hedkwatar Kungiyar a Arusha, Kasar Tanzania.

Ana kyautata zaton cewa zasu tattauna game da gaggauta kafa Tarayyar Gabashin Afirka, yanzu da ya ke Rwanda da Burundi sun shiga cikin Kungiyar yankin.

Haka nan shugabannin ƙasashen za su yi nazari kan wani shirin yin huldar tattalin arziki da Tarayyar Turai, da kafa Kasuwar Yankin Gabashin Afirka da kuma takardar kudi bai daya nan gaba.

XS
SM
MD
LG