Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwannin Zuba Jarin Duniya Sun Fadi


Kasuwannin Zuba Jarin Amurka da na sauran kasashen duniya sun shiga wani halin rashin tabbas, sakamakon barazanar tabarbarewar tattalin arziki da Amurka ke fuskanta, wanda ya jefa masu zuba jari cikin halin rashin tabbas.

Su ma kasuwannin zuba jari na kasashen Australia da nahiyar Asia sun sha kasa da sanyin safiyar Talata, kamar yadda kasuwannin jari barkattai na kasashen duniya suka ji jiki ranar Litinin – duk bayanda aka fara bayyana fargabar cewa tattalin arzikin Amurka na dab da tabarbarewa.

Kusan dukkan ma’aunan mizanin kasuwannin kasashen Asia sun fadi a safiyar yau, yayinda kasuwannin jari na Australia, China, Hong Kong, Japan, Singapore, Korea ta Kudu da Taiwan suma suka yi faduwar tsakanin 4% zuwa 6% a wannan safiyar.

A manyan kasashen Turai da na Asia da na Latin Amurka ma duk kasuwwanin sun sha kasa inda darajarsu ta fadi da tsakanin 3% zuwa 7% a jiya, ranar da masu zuba jari suka yi mummunan asaran da ba safai akanyi irinta ba.

Kan haka ne, daya daga cikin hamshakan attajiran Amurka, George soros jiya yake jan kunnen cewa duniya na fuskantar asarar arzikinta irin wacce ba’a taba ganin mai kamarta ba tun yakin duniya na biyu.

Shima shugaban asusun bada lamuni na duniya na IMF, Dominique Strauss-Khan ya bayyana abinda ke faruwa da cewa “mai muni ne ainun”, inda yace tattalin arzikin kusan daukacin duk kasashen dake bisa doron duniyar nan na fuskantar tashin hankali a saboda wannan lalacewar ta tattalin arzikin Amurka.

XS
SM
MD
LG