Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Wani Gari A Somalia Dake Dab Da Kan Iyakarta Da Kenya.


Rahotanni daga wani gari dake kusa da bakin iyakar Kenya a ƙasar Somaliya sun ce an kashe mutane biyu lokacin da aka kai hari kan wani gini na gwamnati a garin.

Mazauna garin Belet Hawa sun ce wasu mutanen su 9 sun ji rauni a lokacin da wasu ’yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai harin bam a kan ginin cikin daren talata. Mutane biyun da aka kashe masu gadi ne na gwamnatin dake kula da garin. Babu wanda ya ɗauki alhakin kai wannan harin.

Tankiya tana ƙaruwa a bakin iyakar a yayin da tashin hankali mai nasaba da tawayen masu kishin Islama da faɗan ƙabilanci suka yaɗu zuwa cikin ƙasar Kenya. A makon jiya, wasu ’yan bindigar da ake zaton ’yan Somali ne sun sace wasu mata ’yan ɗariƙar Roman Katolika lokacin da suka kai farmaki kan garin El Wak dake bakin iyaka a Kenya suka tsallaka da su cikin Somaliya.

XS
SM
MD
LG