Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Yace Kada Amurka Tayi Maye Fake Da Agana


Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Mr. Kofi Annan, a jawabinsa na karshe kafin ya mikawa magajinsa aiki, yayi wani tattaki mai cike da tarihi, zuwa birnin Missouri, mahaifar tsohon shugaban Amurka Harry Truman, wanda a zamanin mulkinsa ne aka kafa Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1945.

Da yake jawabi ga dimbin mutanen da suka hallara a dakin adana kayan tarihi na Truman, da suka hada da 'yan siyasa da malaman jami’a, Mr. Annan ya jinjinawa kokarin Shugaba Truman na sake farfado da nahiyar Turai bayan yakin duniya na biyu.

Koda yake bai ambaci gwamnatin shugaba Bush ba, Mr. Annan bai boye rashin gamsuwarsa da gwamnatin Amurka maici a yanzu ba, inda yace “Amurkawa sun nuna bajinta a karnin da ya gabata wajen gina kawance mai inganci, wanda ya haifar da Majalisar Dinkin Duniya. Shin burinsu a yau shine na ganin Majalisar Dinkin Duniya ta ragu? Ko kuwa Majalisar Dinkin Duniyar ce bata bukatar gudunmawarsu a yanzu, kamar yadda ta bukace ku shekaru sittin da suka wuce?”

Mr. Annan ya shawarci Amurka da kada ta fake da yakar ta’addanci, ta watsar da kyawawan dabi’unta da aka santa dasu. Mr. Annan yayi ta nanata yabonsa ga Shugaba Harry Truman, wanda yace abin koyi ne ga shugabannin kasashen duniya wajen bin ka’ida da gudun aikin ashsha.

Amurka kadai ya ambata, wajen kira ga kasashen duniya su kare mutuncin kansu, su kuma yi jagoranci da misali. Yace “Amurka ta baiwa duniya misalin dimokradiyya, inda komai karfin mutum la’ifi ne a gaban doka.”

Wakilan Majalisar dokokin Amurka da dama daga Jami’iyyar Republican ta Mr. Bush sun bayyana takaicin kalamun na Mr. Kofi Annan. Shugabn kwamitin hulda da kasashen waje na Majalisar Wakilai mai barin gado, Mr. Henry Hyde yace Mr. Annan bai ambaci “almubazzaranci da rashin tsari a Majalisar Dinkin Duniya ba”.Yace jawabin Mr. Annan misaline na sukar kasar Amurka da bashi da tushe.

XS
SM
MD
LG