Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Koka Da Kashe Mata Minista A Afghanistan


Wa’adin da ‘Yan Taliban suka bayar na a sako masu wadansu mutanensu dake rike a gidan sarka ya wuce, babu kuma wani bayanin samun wani sulhu a tattaunawar da ake dasu. Su dai ‘yan Taliban sunce zasu hallaka mutanen dake hannunsu gaba daya, idan ba a sakar masu mutanen da suke bukata ba.

Jami’an Korea ta Kudu, sun tabbatar da cewa daya daga cikin mutanen dake hannun ‘yan gwagwarmayar, wani Minista dan shekaru 42 mai suna Bae Hyung-Kyu ya mutu, kuma har an gano gawarsa wadda aka yiwa ragaraga da harsasai, a gundumar Ghazmi, a jiya Laraba.

A halin da ake ciki, Ministan Harkokin Wajen Italiya, Massimo D’Alema ya nemi a gaggauta kawo karshen aikin sojin dake karkashin jagorancin Amurka a Afghanistan, saboda abin da ya kira rashe-rashen farar hula na ba gaira ba dalili.

Yace yawan farar hular dake mutuwa a Afghanistan ba karamar annoba bace a siyasance, inda ya kara da cewa kashe-kashen suna kawo zaman dar-dar tsakanin gwamnatin kasar Afghanistan da dakarun kasashen waje dubu 50 dake kasar.

Harbe harben da rundunar NATO, karkashin jagorancin Amurka ke yi, a kokarinsu na kamo ‘yan Taliban, yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan farar hular Afghanistan. Italiya ta bada gudunmawar dakaru dubu biyu ga wannan runduna ta NATO a Afghanistan.

XS
SM
MD
LG