Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben 'Yaraduwa


Juma’ar nan kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin tabbatar da Shugaba Umar Musa ‘Yar Aduwa a matsayin halattaccen Shugaban Kasar, bayan da ta amince da sakamakon babban zaben kasar na bara.

Alkalai hudu daga cikin bakwai ne suka yanke hukuncin watsi da karar da Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar ANPP da Alhaji Atiku Abubakar na AC suka daukaka daga karamar kotun jin kararrakin zaben Shugaban Kasa, suna kalubalantar sakamakon zaben da suka ce an tafka magudi.

Masu duba zaben na kasa da kasa sun rubuta rahotanni dake nuna cewa akwai kura-kurai da dama a zaben na shekara ta 2007, inda aka gaza bude yawancin mazabu a kan lokaci, ‘yan banga da jami’ai kuma suka rika makare akwatunan zabe da kuri’un bogi.

Shi kansa Shugaba ‘Yar Aduwa ya amince cewa akwai kura-kurai a zaben, ya kuma yi alkawarin daukar matakan gyara.

'Yan Najeriya sun baiyana mabambantan ra'ayoyi a kan hukuncin, inda wasu suka ce ya dace, wadansu kuma suka ce babu adalci a cikinsa.

XS
SM
MD
LG