Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Ecowas Na Shirin Kai Dauki Kasar Guinea


Jami’an kungiyar ECOWAS sunce akwai yiwuwar tura wata tawaga da zata iya hadawa da Shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya da Shugaba Abdullahi Wade na Senegal, zuwa kasar Guinea. Ministan Hadin kan Nahiya na kasar Burkina Fasso, Jean De Dieu Somda, wanda ke daya daga cikin masu neman a tura tawagar, yace tashin hankalin da ake ciki a Guinea yana bukatar kulawa ta gaggawa.

Shugaban kasar Guinea, Lansana Conte dai bai sami damar halartar wannan taro ba, saboda halin da ake ciki a kasarsa. Shugabannin Kungiyoyin Kwadago sun bukaci ya sauka, ya kuma kafa gwamnatin rikon kwarya da zata ci gaba da shugabancin kasar. Suka ce Shugaban, wanda ke fama da rashin lafiya, ba zai iya tafiyar da harkokin kasar, har ya warware matsalolin tattalin arziki da take fama dasu a halin yanzu ba.

Mr. Conte dai ya kori Ministansa mai kula da Harkokin Shugabancin Kasa, kuma ya maye gurbinsa da wani na hannun damansa. Ba a dai san dalilin daukar wannan mataki ba. Saidai, Shugabannin kwadagon sunce wannan kwaskwarima ba zata wadatar ba, inda suka tsaya a kan bakansu cewa lallai Mr. Conte ya sauka daga mukaminsa.

Bayan rikicin nan na kasar guinea, maganar kasar Ivory Coast ma ta ja hankalin shugabannin kasashen na Africa ta Yamma, inda suka yaba wa Shugaba Luarent Gbagbo, saboda kokarinsa na sasantawa da ‘yan tawayen kasarsa dake rike da yankin arewacin kasar. A da, Mr. Gbagbo ya zargi kungiyar ta ECOWAS da kasa yin wani katabus wajen tabbatar da hadin kan kasarsa.

Shugaban ECOWAS mai barin gado, Shugaba Tandja Mamadou na Jamhuriyar Nijar, ya nemi shugabannin kasashen, da kada wannan halaiya ta Ivory Coast ta kashe masu guiwa.

XS
SM
MD
LG