Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lansana Conte Ya Mutu: Gunea Ta Shiga Rikici


Da sanyin safiyar yau Talata kasar Guinea ta shiga sabon rikici, bayan da aka baiyana rasuwar Shugabanta Lansana Conte.

Ba tare da wani bata lokaci ba, Kyftin Moussa Camara yayi jawabi ta kafofin yada labarai cewa sojoji sun dakatar da tsarin mulkin kasar, sun kuma rushe dukkan kafofin gudanar da mulki na kasar. Yace an maye gurbin gwamnatin da Majalisar Tuntuba ta soji, wacce zata tafiyar da mulkin kasar.

Kamfanin Dillancin Labari na Associated Press, ya ruwaito daga Guinea cewa Jami'in sojin ya baiyan cewa za a gudanar da babban zaben kasa nan ba da dadewa ba.

Har yanzu dai babu bayanin cewa Camara shine jagoran juyin mulkin ko kuwa kakain sojojin ne kawai.

Kafin sojojin su karbe ragamar shugabancin kasar, har Shugaban Majalisar kasar ya umarci Kotun Koli ta bi ka'idojin tsarin mulki, ta baiytana shi a matsayin sabon shugaban da zai maye gurbin Shugaba Conte.

Jiya Litinin Shugaba Lansana Conte ya mutu, bayan ya sha fama da rashin lafiya. Ba a dai tabbatar da hakikanin shekarunsa ba, amma bayanai sun nuna cewa yana da shekaru saba'in da 'yan kai.

Koda yake ba a tantance musabbabin mutuwar tasa ba, makusantansa sunce yana fama da ciwon suga (diabetes), gashi kuma da shan taba sigari.

Shugaba Conte ya zama shugaban kasa, bayan ya kwace ragamar mulki, a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini ba, da ya yiwa Shugaban farko, Ahmed Sekou Toure. Shi kansa Sekou Toure ya rasu a shekarar 1984.

XS
SM
MD
LG