Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gurbataccen Maganin Fitar Hakori Ya Kashe Yara Ashirin Da Biyar A Najeriya.


Jami'an Najeriya sun ce yara ashirin da biyar sun mutu sakamakon amfani da maganin hakori. Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya ko NAFDAC a takaice tace, maganin mai suna "My Pikin" "ko jariri na" an yi shi ne da nufin magance ciwon fitar hakori.

Amma jami'ai suka ce maimakon amfani da hade hade da aka amince da su wajen yin magananin,masu maganin sai suka hada da abinda ake kira diethlyne glycol,da ake amfani dashi wajen hada ruwan lagireto da ire irensa. Jami'ai suka ce an rufe kamfanin da ya ke yin maganin mai suna Barewa Pharmaceautical,hukumar tana kuma kira ga iyaye kada su baiwa yaransu wannan magani.

NAFDAC tace an sami rahoton mace macen ne daga asibitoci a Legas,Zaria,da kuma Ibadan. Haka kuma sun bada labarin akalla yara 30 an kwantar da su a asibiti da cutar koda,bayan sun kamu da zazzabi,amai da kuma gudawa.

XS
SM
MD
LG