Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Mai Ya Fadi A Kasuwar New York A Hada-Hadar Yinin Talata.


Farashin ɗanyen mai ya yi ƙasa yau a kasuwannin birnin NY. Farashin ya sauka da kimanin dala biyu inda aka sayar da ɗanyen mai a kan dala 52 da senti sittin da biyar kan kowace ganga.

Jiya Litinin farashin gangar ɗanyen mai ya cira da misalin sama da dala huɗu a lokacin rufe kasuwannin bayanda gwamnatin amurka ta sanar da ba bankin Citigroup dake neman durƙushewa rancen biliyoyin dala.

Masu kula da lamura suna kyautata zaton farashin ɗanyen mai zai ci gaba da faɗuwa yayinda faɗuwar tattalin arziki ya tilasta rage bukatar mai.

XS
SM
MD
LG