Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka Zata Amince Da Wasu Makudan Kudaden Don Farfado Da Tattalin Arziki


Shugaban Amurka Barack Obama yace yana sa ran Majalisar kasar zata amince da wani shirin da ya gabatar da farfado da tattalin arzikin kasar, da ya shiga mawuyacin hali.

A yau Juma'a ya gana da shugabannin jam'iyyun Democrat da na Republican, inda ya jawo hankulansu cewa tattalin arzikin kasar ya shiga wani mawuyaci hali.

Yace shirin nasa na tada komadar tattalin arziki, zai samar da sabbin aiyuka miliyan uku zuwa hudu, ya kuma ce Majalisar ta shirya amincea da shirin.

Shugaba Obama ya kara jaddada muhimmancin gaskiya da rikon amana, domin tabbatr da cewa shirin na tada komadar tattalin arziki bai baude ba.

A yau din dai kuma Shugaba Barack Obama ya sanya hannu a kan wani umarni dake janye haramcin tallafawa kungiyoyi masu zaman kansu dake taimakawa a zubar da ciki.

Dokar da aka soka din, ta hana gwamnatin Amurka bada gudunmawa ga kungiyoyin kaiyade iyali na kasashen waje, muddin dai suna goyon bayan zubar da ciki, koda kuwa ta hanyar bada shawara ne.

XS
SM
MD
LG