Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattijai Ta Najeriya Ta Yi Muhawara Kan Rashin lafiyar Shugaba Yaradua


Majalisar Dattijai Ta Najeriya ta tafka muhawara na tsahon sa'o'i shida a asirce gameda rashin lafiyar shugaban Umaru Musa 'Yaradua,da bukatar a bi tsarin mulkin kasa. Wakiliyar Sashen Hausa a Majalisar ta lura cewa fuskokin wakilan yana murtuke,babu alamar sun saki jiki.

Da yake magana kan zaman,senata Suleiman Nazif yace sun tattauna kan bukatar mutunta tsarin mulki a gefe daya kuma,an tausayawa shugaban kasar ganin ya tafi neman jinya ne,kuma kamar yadda yace ya fara samun sauki.

Ahalin yanzu kuma, tsoffin 'yan takarar shugaban kasa a zaben da ya shige,ciki har da Janar Muhammadu Buhari na Jam'iyyar ANPP, sun yi taro a legas kan matsalar rashin lafiyar shugaban kasar,da gibi da haka ya haifar.

XS
SM
MD
LG