Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tace A Mayar da Yaran Chadi Gida


Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya yace akwai bukatar yaran nan da wata kungiyar agaji ta Faransa ta so ta sace daga Chadi, so sadu da iyayensu cikin gaggawa.

Mataimakin Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira, L. Craig Johnstone, shine ya bayar da wannan sanarwa, bayan ya ziyarci gidan marayun da ake kula da yaran, a garin gabashin Chadi na Achebe.

A ranar Talata Hukumar ta majalisar Dinkin Duniya mai Kula da Makomar ‘Yan Gudun Hijira, tace bisa dukkan alamu, yaran suna cikin matukar bukatar komawa ga iyayensu, kuma lallai a mayar dasu gida, ko a takaita halin tashin hankalin da suke ciki.

A watan jiya hukumomin Chadi suka hana wata kungiyar agaji ta Zoe’s Ark fita da yara 103 zuwa Faransa, domin abin da suka ce wai zasu sama masu iyayen rana ne.

XS
SM
MD
LG