Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makiyaya sun addabi Namun Daji A Uganda


Masana harkokin gandun daji a Uganda sunce suna zaton wadansu makiyayan nshanu ne suka sanyawa zakoki da sauran namun daji guba a gandun dajin Sarauniya ‘Yaz Zabil (Elizabeth).

Jami’an gandun dajin suka ce yawan zakokin dake dajin sun ragu matuka, daga guda 94 a shekarar 1999, zuwa 39 a yau. An kashe a kalla 10 cikin watanni 15 da suka wuce.

Wani likitan dabbobi dake koyarwa a Jami’ar Makerere yace makiyayan suna zubawa namun dajin guba ne saboda su hana su kashe masu shanu.

A bara aka kyake kimanin makiyaya dubu 10 daga kabilar Basongora su zauna a gefen dajin na dan wani lokaci. Amma jami’an gandun dajin sunce makiyayan sun fara keta iyakokinsu.

Hukumar gandun Daji ta Uganda tace idan dai aka kyale wadannan zakoki suka kare, to kwarjinin dajin zai zube a idanun ‘yan yawon bude idanu.

XS
SM
MD
LG