Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kasashen Duniya Masu Hanu Da Shuni Suna Taro A Washinton Kan Matsalar Tattalin Arzikin Duniya


Jumma'an nan, shugabannin Kasashe Masu Arziki suna tinkarar sashen kudi na Duniya da ya durkushe,yayinda suka hallara anan Washington,domin magance faduwar kasuwannin hannayen jari,tsaida bada rance,da fargabar tattalin arzikin Duniya ya tashi durkushewa baki daya.

Kasuwar saida hannayen Jarin Amurka ta fadi da kamar kashi biyar cikin minti biyar da budewa a yau,bayan mummunar hasar da kasuwar ta tafka jiya Alhamis.

Manyan kasuwannin saida hannayen jarin kasashe dake Turai, sunyi kar da kamar kashi tara zuwa 10 a hada-hadar zuwa tsakar ranar Jummaa. A Rasha hukumomi sun tsaida hada-hadar kasuwannin hannayen jarin kasar biyu har sai illa ma Sha Allahu.Kasuwar saida hannayen jarin Nikkei,ta Japan ta fadi da kusan kashi 10 a karshen cinikin yau, faduwa mafi girma da ta gani a yini daya tun 1987.

Jami'ai daga kasashe masu arzikin masana'antu bakwai,Amurka,Japan,Britaniya,Jamus,Faransa,Canada da Italiya,sun hallara anan Washington,gabannin taron Asusun Bada Lamuni,watau IMF ,daga bisani kuma su gana da shugaban Amurka George Bush, Asabar idan Allah ya kaimu. Dazun nan ne Shugaba Bush, yayi tsokaci gameda matsalar kudi da ake fuskanta ahalin yanzu.

XS
SM
MD
LG