Accessibility links

Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney Ya Kai Ziyarar Bazata Afghanistan


Dazune mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney ya tattauna tare da shugaba Hamid Karzai na Afghanistan bayan isarsa birnin Kabul a wata ziyarar ba zatan da ya kai.

Mataimakin shugaban na Amurka Cheney ya shaidawa manema labarai cewa Amurka da kawayenta na bukatar kafa wata rundunar soja mai karfin gaske a Afghanistan wadda zata iya tabbatar da ayyukan tsaro. Ana kuma kyautata cewar mataimakin shugaban Amurka Cheney zai ziyarci sansanin rundunar sojin Amurka domin yi masu jawabi a Afghanistan.

XS
SM
MD
LG