Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Niger Deltan Najeriya Sun Sake kai Hari


Hukumomin Najeriya sunce wadansu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu, a lokacin da suke kokarin sace wadansu ma’aikatan kasashen waje, a birnin Fatakwal .

dake yankin Niger Delta a yau Juma’a. Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar rivers yace ‘yan bindigar wadanda ke sanye da kayan sojoji, sun farwa wani jerin gwanon motocin dake rakiya ga ma’aikatan kasasahen wajen zuwa wajen aiki. Saidai ‘yan bindigar basu sami damar satar koda mutum daya ba.

Tsagerun Niger delta dai sun sha kaiwa kamfanonin mai a yankinsu hari, inda suke sace ma’aikata, musamman ma ‘yan kasashen waje. Yawancin masu satar dai sunce suna kokawa ne na nemawa yankin nasu karin kaso daga dukiyar man fetur da ake samu, amma kuma wadansu sunce ‘yan banga ne kawai da suka mayar da irin wadannnan hare hare hanyar samun kudi a bagas.

Hare haren dai sunyi illa ga aikin hakan mai a Najeriya, saboda yawancin ma’aikata ‘yan kasashen waje sun kauracewea yankin.

XS
SM
MD
LG