Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sauara Kwanaki Tara Amurkawa Su Tafi Rumfunan Zaben Shugaban Kasa, 'Yan Takara Suna Kara Matsa Kaimi Domin Tabbatar Ganin Sun Sami Nasara.


‘Yan takarar shugaban Amurka biyu John McCain da barack Obama sun haɗu yau a jihar Virginia mai sarƙaƙiya wajen fahimtar kamun ludayin siyasarsu, domin duk wanda suka nuna amincewa gareshi da alamar shine zai sami nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa, a zaɓen huɗu ga watan Nuwamba.

Dukkan ’yantakarar biyu sun kammala gangamin zaɓensu jiya a jihohin Pennsylvania da Ohio. Jami‘an gangamin zaɓen Obama sun ce a gangamin zaɓen Virginia ne ake sa ran Obama zai fasa ƙwai.

Shi kuma John McCain yace zai ci gaba da hoɓɓasa har ya kai ga samun nasara duk da alamar koma bayan da alƙaluman ƙididdigar ra’ayin masu kaɗa ƙuri‘a ke nunawa.

XS
SM
MD
LG