Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar 'Yan Hamayya MDC A Zimbabwe Tana Taron Koli Domin Tsaida Shawarar Ko Ta Shiga Gwamnatin Hada Kan Kasa


Jam’iyyar hamayya ta Zimbabwe MDC tace an fara tattaunawar ƙolin a tsakanin shugabanni da ’ya’yan jam’iyyar kan dacewa ko rashin da cewar shiga Gwamnatin haɗin ƙasa tare da shugaba Robert Mugabe.

Mai magana da yawun jam’iyyar ta MDC Nelson Chamisa, yace a yau juma’a aka fara tattaunawar da ake ganin za’a shafe yini guda ana yi. Ya kuma zargi jam’iyyar ZANU-PF ƙarƙashin jagorancin Mugabe da laifin rashin sanin alƙiblar daza’a bi, da fatan shugaba Mugabe zai yi aiki da sharuɗɗan da taron ƙolin shugabannin kudancin Afirka suka shimfiɗa domin samun nasarar sabuwar Gwamnatin haɗin kan ƙasar Zimbabwe.

XS
SM
MD
LG