Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mexico Ta Gamu Da Bala’in Ambaliyar Ruwa


Gwamna Jihar, Andres Granier yace kimanin mutum dubu 300 suke jiran a ceto su, daga abin da ya baiyana a matsayin mummunan halin da suke ciki.

A kalla mutum miliyan daya, rabin yawan al’ummar jihar ne suka sami tabuwa daga ambaliyar ruwan. Hotuna sun nuno mutane suna ta kokarin kara yin sama, a lokacin da ruwa yake toroko, yana shan kansu a inda sukai mafaka.

An ciccika buhuna da yashi an shinge wurare da dama, amma da ruwan ya zo, sai kawai ya mamaye su. Kimanin kashi 80 bisa dari na Tabasco, na karkashin ruwa a halin yanzu, kuma gwamnan yace jihar tayi asarar ilahirin amfanin gonarsu na bana.

An dai sami mace mace, a wannan ambaliyar ruwa da shugaban Kasa Felipe Calderon yace tana daga cikin annoba mafi muni da suka taba samun kasar. Ya bukaci jama’ar Mexico su aike da gudunmawar ruwan sha da abincin gwangwani, kayan masarufi, da suturu ga wararen da aka tanada domin karbar gudunmawa.

XS
SM
MD
LG