Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Murar Tsuntsaye Ta Kashe Mutum Na Farko A Najeriya


Jami’ai suka ce wata mace mai shekaru 22 da haihuwa wadda ta mutu ranar 17 ga wannan wata a Lagos ita ce ta farko da aka tabbatar a Nijeriya. Suka ce ana jinyar wani dan’uwa, ko ’yar’uwar wannan mace a wani asibitin lagos mai dauke da wannan cuta ta murar tsuntsaye.

Har yanzu babu sakamako mai gamsarwa dangane da gwaje-gwajen da aka yi kan wasu mutanen su ma ake kyautata zaton suna dauke da wannan cuta.

Wani jami’in kula da lafiyar jama’a a Nijeriya, Dr. Abdulsalam Nasidi, ya fadawa Muryar Amurka cewa gwamnati zata kaddamar da wani gagarumin gangamin kiwon lafiya domin dakile yaduwar wannan cuta.

Har yanzu dai wannan kwayar halittar cuta mai haddasa murar tsuntsaye, halitta ce dake yaduwa a jikin dabbobi, amma kuma tana iya kama mutumin da ya kusanci tsuntsaye dake dauke da ita.

XS
SM
MD
LG