Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Janye Tuhumar Leken Asirin Kasa Daga Kan Judith Asuni


Gwamnatin Tariyar najeriya ta janye tuhumar da take yiwa Ba’amurkiya Judith Burdin Asuni da Dan Najeriya Danjuma Saidu har ma da wadansu da jamusawa biyu masu aikin fina finai.

Wani babban Lauyan Gwamnati Salihu Aliyu ya gayawa manema labaru ranar Laraba a Abuja cewa shawarar watsi da tuhumar abu ne da ya dace da bukatun kasa.

An tsare Judith Asuni Ba'amurkiya tareda Danjuma Sai’du an ranar 26 ga wata, bisa zargin taimakwa yan kasar Jamaus biyu su dauki hotunan wasu muhimman cibiyoyin mai a yankin Niger Delta, kuma suka gaya musu kariyarda zasuyi domin a basu visar zuwa Najeriya.

Dukkan su hudu sunki amsa laifi da ake tuhumarsu akai.

Ita dai Asuni Babbar Darekta ce ga Academic Associates, wata kungiya mai zaman kanta a Najeriya. Tana auren dan Najeriya kuma ta zauna a najeriya har na tsawon shekaru da dama.

Kungiyar tana aikin shiga tsakanin tsagerun Niger delta da Gwamnati.

XS
SM
MD
LG