Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Lashi Takobin Farfado Da Darajar Naira


Babban Bankin Najeriya yace kasar zata kara darajar kudinta na Naira, domin rage hauhawar farashin kayayyaki.

Babban bankin yace wannan mataki zai fara aiki daga watan Agustan badi, kuma zai sauko da farashin kayayyaki, sannan ya saukaka wa mutane daukar kudi mai yawa.

Kansuwannin Najeriya basa ta’ammali da irin katin nan da ake amfani dashi wajen cinikaiya a kasashen waje, wanda yakan sanya mutane daukar makudan kudade a duk lokacin da zasu yi ciniki.

Babban bankin na Najeiya yace kara darajar nairar, zai kuma dawo da martabar karafan kwabbai da siyasa, ya kuma saukaka musayar kudaden kasashen waje.

A yanzu ana musayar dollar Amurka daya da Naira 128, amma idan aka daga darajar nairar, dollar Amurka zata fado zuwa naira daya da kobo ashirin da biyar.

XS
SM
MD
LG