Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Musanta Hannu A Harin Fadar Shugaban Kasar Equatorial Guinea


Cece-kucce ya barke a Nigeria a tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar tsageru ‘yantawayen yankin Niger Delta, inda kowanne ke zargin dayan da cewa shine ya haddasa farmakin da aka kai akan fadar shugaban kasar Equatorial Guinea.

Ita kanta Equatorial Guinea, ta fi zargin 'yan bindigar kungiyar tsageru ta MEND ne da laifin kai farmakin. Ministan Harakokin Wajen Nigeria Ojo Maduekwe yace Zata iya yiyuwa wadanda suka kai farmakin daga Nigeria suka fito, amma kuma yace bai yanke kaunar cewa su sojan haya ne da aka dauko ma daga wasu sassan Afrika daban-daban ba.

Ministan yace Nigeria na Allah-waddai da harin, ko ma waye ya kai shi. To amma wani kakakin ‘yantawayen na Niger Delta yace su ba ruwansu da maganar wannan farmakin, yace gwamnatin Nigeria ce ta shirya kai shi har ma ta dauko su mayakan a matsayin sojan haya, ta ingiza su suka afkawa fadar ta shugaban kasar ta Equatorial Guinea.

Har zuwa yanzu dai ba’a san dalilin kai harin ba. Birnin Malabo na Guinea, inda fadar da aka kaiwa farmakin take dai, duka-duka kilomita 200 ke tsakaninsa da Fatakwal dake can kudancin Nigeriar.

XS
SM
MD
LG