Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Binciki Tsohon Shugaba Obasanjo


Hukumar hana al-mundahana ta Nigeria, EFCC, tace ta soma gudanarda bincike akan tsohon Nigeria, Olusegun Obasanjo.

A hirar da tayi da Sashen Hausa na VOA, shugabar hukumar Farida Waziri ta tabattarda cewa lalle suna gudanarda binciken mundahanar da ake jin kila Obasanjo ya aikata a lokacin mulkinsa.

Masu sukar lamirin Obasanjo din na zarginsa da baiwa ‘yanuwansa da na kusa da shi manyan kwangiloli masu tsoka a lokacin mulkin nashi na shekaru 8, sai dai tsohon shugaban ya musanta zargin.

Haka kuma Farida Waziri ta tabattarda gaskiyar rahotanin dake cewa takardun binciken da ake akan wasu tsofaffin gwamnonin jihohi 31 duk sun bace, don haka ita ba ta yadda zata iya bincikarsu.

Ta wani abinda ya shafi Nigeria din har ila yau, lauyan wani mawallafi kuma dan jarida dan Nigeria dake zaune a nan Amurka, Jonathan Elendu, da aka cafke bayanda yaje can Nigeria, ya nemi ‘yan sandan dake tsare da shi da ko dai su sake shi ko kuma su tuhume shi da aikata wani laifi.

Tun ran 18 ga watan nan na Oktoba ake tsare da Mr. Elendu bayan da ‘yan sandan-ciki suka cafke shi da saukarsa a filin jirgin saman Abuja bayan isowar sa daga nan Amurka.

Kan haka ne, lauyansa dake zaune a Lagos, Festus Keyamo yayi kira akan ‘yansanda suyi aiki da dokokin Nigeria da suka ce in an kama mutum, dole a sake shi ko kuma a tuhume shi da wani laifi kafin cikar sa’oi 24 da kama shi.

Su dai hukumomin na Nigeria sun zargin Mr. Elendu da laifin bata sunan Nigeria da kuma bada labaran dake barazana ga zaman lafiyar kasar.


XS
SM
MD
LG