Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Tsagerun Niger Delta Suna Barazanar Tada Husma


Babbar kungiyar tsagerun yankin Niger Delta tana barazanar haddasa mumunar fitina cikin yankin, idan ba ayi adalci kan batun tuhumar cin hanci da rashawa da akeyiwa wasu jamiai cikin yankin.

Talata hukumar yaki da masuyiwa tattalin arziki zagon kasa, EFCC, ta bada sanarwar kama babban jami’in kula da harkar mulki na Gwamnan Jihar Rivers,Nyeson Wike,da sakataren Gwamnatin Jihar Magnus Abe, saboda zargin su da almubazzaranci.

Cikin sanarwa da kungiyar MEND ta bayar yau Laraba,tace tana sa ido kan maganar sosai,saboda bata amincewa Gwamnati ba,domin sai tayu a saki jami’an ba tared anyi musu hukunci ba. Kungiyar tace idan bata gamsu da yadda aka tafiyar da da batun ba,zata haddasa mummunar rashin zaman lafiya a Jihar Rivers.

XS
SM
MD
LG